Labarai
Za mu yi bincike kan gine-gine da filayen da aka yanka a Dawakin Tofa- Kantoma
Gwamnatin jihar Kano ta umarci duk wani wanda yasan ya fara gini ko yanka gonaki da suke mallakin gwamnati a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ya dakata domin gwamnati zata gudanar da binciken yadda aka mallaka musu.
Shugaban ƙaramar hukumar na riƙo Kabiru Ibrahim Danguguwa, ne ya bayyana hakan yayin rabon tallafin kuɗi ga dukkan nin shugabancin ƙaramar hukumar domin samar musu da abin da zasu gudanar da bikin sallah.
Kabiru Danguguwa ya kuma ce wannan mataki na dakatar da duk wasu masu gine-gine ko yanka gonaki da filaye Asibitoci da makarantu ya biyo bayan bincike da gwamnatin Kano zatayi kan yadda gwamnatin baya ta mallakawa su gurare mallakin gwamnati.
Ɗanguguwa ya ƙara da cewa yanzu haka gwamnati jihar kano ta samar da wani kwamiti wanda zaiyi binciken yadda akayi tasarrafi da filaye da gonakin gwamnati a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.
Haka kuma zamu ɗau mataki ga duk wanda muka samu da yin kunnen ƙashi wajen ƙin dakatar da gini ko yanka filaye a yankin, A cewar Ɗanguwa.
You must be logged in to post a comment Login