Labarai
Za’a daga matsayin tashar wutar lantarki ta jihar Yobe
Gwamnatin tarayya zata daukaka matsayin tashar yada wutar lantarki ta jihar Yobe domin fadada ta yadda zata iya samar da karin wutar lantarki da zata wadaci al’ummar jihar Yobe.
Ministan lantarki Injiniya Abubakar D. Aliyu ne ya bayyana hakan yau labara yayin ziyarar gani da ido a babbar tashar wutar lantarki ta jihar Yobe dake babban birnin jihar Damaturu.
Ministan wanda shugaban kamfanin raba wutar lantarki na kasa wato TCN Injiniya Sule Abdulazeez ya wakilta, ya kuma ce karuwar bukatar wutar lantarki a yankin ya nuna tashar wutar lantarki tana bukatar a daga matsayinta.
“An bada kwangilar samar da naurar da zata kara yawan wutar lantar mai karfin Volt-Amps (MVA) miliyan 150 a tashar wutar lantarkin ta jihar Yobe,” inji ministan.
Injiniya Abubakar D. Aliyu ya yabawa hukumomin tsaro saboda kokarinsu wajen samar da tsaro ga tashar wutar lantarki
Minis yayi kira ga jama’ar dake kusa da tashar wutar lantarkin su kula da ita domin ta ci gaba da amfanar al’umma baki daya.
A watan Fabrairu na 2019 ne shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da babbar tashar wutar lantarkin da take Damaturu babban birnin jihar Yobe.
You must be logged in to post a comment Login