Manyan Labarai
Za’a fara darusan yaki da rashawa a jami’ar ABU
Mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC lbrahim Magu ya ce kwalejin hukumar zata samar da kwasa-kwasai kan yadda za a dakile cin hanci da rashawa a cikin al’umma.
Ibrahim Magu ya ce wannan na daga cikin dimbin hanyoyin da hukumar ta bullo da su don yaki da cin hanci da rashawa a kasar nan.
Magu ya bayyana hakan ne yayin sanya hannu kan yarjejeniyyar fahirmtar juna da jamiar Ahmadu Bello dake Zari’a.
Da dumi-dumi: EFCC ta cafke Muntari Ishaq Yakasai
Hukumomi kadai ba za su iya magance cin hanci da rashawa ba- EFCC
Hukumar EFCC za ta fara gurfanar da Angwaye a Kotu
Yarjejeniyyar za ta sanya kwalejin hukumar yaki da cin hanci da rashawa dake Karu a babban birnin tarayya Abuja da kuma jami’ar samar da kwasa-kwasai na yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifuka.
Da yake jawabi tun da fari, shugaban jami’ar ta Ahmadu Bello Farfesa Ibrahim Garba ya ce shakka babu yarjejeniyyar tsakanin jami’ar da kwalejin zata taimaka wajen cike gibin da ake da shi wajen yaki da wannan ta’ada.
You must be logged in to post a comment Login