Manyan Labarai
Za’a magance matsalar titi a Tarauni- Hafiz Kawu
Korafin da al’ummar mazabun unguwa UKU cikin gari da kauyen Alu ke yi na rashin kyawun titin da ya tashi daga Tsamiyar mashaya zuwa tashar unguwa uku, ya fara zama tarihi biyo bayan fara aikin titin da dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Tarauni Hafiz KAWU ya bayar.
Mazauna yankunan dai sun ce rashin kyawun hanyar ta janyo musu shiga halin tasku tsawon lokaci da dama.
“Hajiya Halima Muhammed Limawa daya ne daga cikin iyaye mata da ke mua’amala a titin da ya tashi daga tsamiyar mashaya a kullu yaumin, ta shaiwada freedom rediyo cewa suna shiga mawuyacin halin a duk lokacin damina sanadiyar rashin kyawun titin”.
‘‘Titin wanda tun farko aka samar dashi kusan shekaru ashirin da suka gabata, ya bukaci gyara amma gwamnati-bayan gwamnati sun zo ba tare da samun nasarar magance shi ba’’, a cewar Hajiya Limawa.
A yayin wata ziyarar da tashar Freedom rediyo ta kai wajen da ake gudanar da aikin, wasu daga cikin al’ummar yankunan sun ce gyara musu titin a wannan lokaci, zai dauke musu daya daga cikin manyan kalubale da ke addabarsu.
Yadda al’ummar Dawakin Kudu suka koka kan matsalar hanya
An daidaita tsakanin KAROTA da ‘yan kasuwa bayan dakatar da tsayawar Tireloli akan titi
“Sun ce a sau da yawa, sun sha kaiwan korafi kan titin ga hukumomi amma ba a daukar mataki, shi yasa wannan karon su ke fata ganin an kammala aikin kamar yadda ya kamata”.
Alhaji Hassan Yahaya Kila shine wanda ya wakilci dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Tarauni Alhaji Hafiz Kawu wajen duba aikin, ya shaidawa manema cewa, nan ba da dadewa ba za a kammala kwaskwarima ga titin kafin daga bisani ayi mai aiki mai gaba daya.
“Ina tabbatar da muku tuni an sa aikin cikin ayyukan mazabu na dan majalisar tarayyar ta Tarauni kuma nan ba dadewa ba za’a fara aikin gadan-gadan shi yasa muka fara yin kwaskwarima don ragewa al’umma wahalhalun da suke fuskanta a wannan lokaci na damina”.
You must be logged in to post a comment Login