Labaran Wasanni
Za’a rinka sauya ‘yan wasa sau 5 a gasar Bundesligar Jamus
Shugaban hukumar shirya gasar Bundesligar kasar Jamus, Christian Seifert, ya ce kungiyoyin kwallon kafar dake buga gasar za su rinka sauyin ‘yan wasa sau biyar a wasa mai makon sau uku da ake a baya kafin zuwan cutar Corona.
Christian Seifert, ya ce dokar za ta fara aiki a kakar wasanni mai kamawa ta shekarar 2020/2021.
Ya kuma ce hakan ya biyo bayan matakai da hukumar shirya gasar ta Bundesliga ta dauka domin kaucewa yaduwar cutar Corona ga ‘yan wasa.
Hukumomin kwallon kafa a nahiyar Turai dai, tuni suka fara aiwatar da wannan dokokin tun daga bullar cutar ta Corona ciki kuwa harda kasar ta Jamus, sai dai sun bayyana cewa dokar za ta yi aiki ne kawai har a karkare gasar cin kofin kasar ta Jamus.
Tuni dai hukumar kwallon kafa ta kasar Jamus ta bayyana sauyin ‘yan wasa sau 5 a wasannin kwallon kafa daban-daban na fadin kasar da suka hadar da ta mata da kuma ta maza.
Za dai a dawo gasar cin kofin Bundesliga a ranar 18 ga watan Satumba, inda zakarar gasar a bana Bayern Munich za ta fafata da Shalke 04 a wasan farko.
Sai dai ta ce babu tabbacin barin ‘yan kallo zuwa filayan wasannin kamar yadda aka saba kafin zuwan Corona, sai dai za’a rage yawan masu zuwa kallo domin gudin cakuduwa.
Tuni dai aka sahalewa kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig da ta shigar da ‘yan wasa 8,400 a wasan ta na farko da za ta yi da Mainz 05 a ranar 20 ga watan Satumba.
Haka ita ma kungiyar Hertha Berlin an sahale mata da ta shigar da ‘yan kallo 4,000 a wasanta na farko kwanaki biyar bayan wasan RB Leipzig.
You must be logged in to post a comment Login