Kiwon Lafiya
Majalisar zartaswa ta amince da fitar da Naira Miliyan 977don samar wa hukumar fasa kwauri muhalli
Majalisar zartaswa ta amince da fitar da Naira Miliyan dari tara da saba’in da Bakwai, domin samar wa ma’aikatan hukumar fasa kwauri ta kasa muhalli.
Ministar kudi Zainab Ahmad ce ya bayyana haka, yayin zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala zaman majalisar a daren jiya, wanda shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta.
Zainab Ahmad ta kuma ce, samar da muhalli ga ma’aikatar hukumar na da muhimmanci sosai, a don haka ma’aikatar kudi ya ga dacewar samar tare da inganta muhallansu.
Ka zalika Zainab ta ce, hukumar ta kuma samu sahaliwar fitar da kudade don sayar kayayyakin sadarwa na zamani, wanda suka hada da Nau’rorin kwamfuta da Rediyoyin zamani.
Tana mai cewa kayayyakin zai taimaka gaya, wajen musu tafiyar da ayyukan yadda ya kamata.
A nasa bangaren Ministan Birnin tarraya Abuja Muhammad Bello ya ce, majalisar ta kuma amince da bada kwangilan gina titunan cikin birni, daga Dangara zuwa titin Yaba a unguwar Kwali da ke Birnin tarraya Abuja.
Ministan ya kuma ce, za a baiwa ‘yan kwangilar damar sayan kayayyakin ayyukan gyara titin, wanda zai lakume Naira Milliyon dari Bakwai da dari Biyu da Ashirin da biyar.