Labaran Kano
Farashin shinkafa zai karye- Kamfanonin sarrafa shinkafa
Kungiyar masu kamfanonin sarrafa shinkafa da takwararsu ta ‘yan kasuwa sun sha alwashin yin duk me yiwuwa don ganin farashin shinkafa ya sauko a nan jihar Kano dama kasa baki daya.
Masu kamfanonin shinkafar da ‘yan kasuwar sun yi wannan alwashi ne yayin wani taro da suka gudanar da hukumar yaki da fasakwauri ta kasa kwastam da kuma hukumar tsaro ta sirri ta kasa (DSS), yau a nan Kano.
Sun ce, bako shakka akwai matsaloli da rashin fahimta tsakanin ‘yan kasuwa da kuma masu kamfanonin sarrafa shinkafa a nan Kano wanda hakan yana taimakawa wajen hauhawar farashinta, amma za su yi duk me yiwuwa wajen ganin an samu mafita wanda zai taimaka wajen sauko da farasahin shinkafar.
Nan bada jimawa za’a fara fitar da shinkafa zuwa ketare -Nanono
Za’a dawo da ma’aikatun casar Shinkafa a Kano -Nanono
RIPAN: An yi fasakwaurin shinkafa cikin kasar nan da ya kai sama da tan Miliyan daya
Tun farko da ya ke jawabi, shugaban hukumar yaki da fasakwauri ta kasa kwastam mai kula da shiyyar Kano da Jigawa, Nasir Ahmed, ya ce, makusudin shirya taron shine domin nemo hanyoyin dakile fasakwaurin shinkafa da kuma dakile hauhawarta ba bisa ka’ida ba.
Taron dai wanda aka gudanar da shi a ofishin hukumar tsaron sirri ta DSS da ke nan Kano, ya kuma nemi hadin kan ‘yan kasuwar domin rufe duk wata kafa da za ta taimakawa masu safarar shinkafa shigo da ita kasar nan.