Labaran Wasanni
Za’a yiwa ‘yan wasan dake buga gasar premier ta kasa gwajin Corona-Sunday Dare
Ministan Matasa da Wasanni, Sunday Dare, ya ce Kungiyoyin dake buga gasar Premier ta Kasa dole ne a yi musu gwajin cutar Corona kafin dawowa ci gaba da gasar a nan gaba.
Tsawon watanni uku Kenan da aka tafi hutun gasar premier ta kasa sanadiyyar bullar cutar Corona a kasar nan.
Sunday Dare ya bayyana hakan ne a yayin da yake tattauwa da wata kafar yada labarai a jiya Alhamis, a nan Najeriya, kan yiwuwar bude wasanni a filayen wasanni dake fadin Kasar nan.
Sunday Dare ya kuma bayyana cewa ‘yan wasa da masu horos dasu za’a tabbatar da lafiyar su kafin amincewa da ci gaba da buga wasanin gasar premier din.
Ko Real Madrid za ta iya daukan Laliga?
Dalung tells NFF to Pay Siasia
A cewar sa irin hakan ne ya faru a gasar Bundesliga ta kasar Jamus kafin amincewa a dawo ci gaba da gasar, sai da aka gwada dukkan wani dan wasa da masu kula dasu kuma aka tabbatar basa dauke da cutar sannan aka amince da a ci gaba da gasar.
Ya kuma ce a yanzu haka ana nan ana gwada ‘yan wasan dake buga gasar Laligar kasar Spaniya dana Seria A din kasar Italiya a shirye-shiryen da ake na dawowa gasar.
A cewar sa, ba za su bari lafiyar yan wasa ya shiga garari ba, domin lafiya ita ce komai a don haka hukumar shirya gasar premier da hukumar wasanni ta kasa dasu tabbatar da hakan.
You must be logged in to post a comment Login