Manyan Labarai
Zaben 2023: Ba zan sake tsayawa takara ba- Shugaba Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari yace tsarin mulkin Najeriya bai ba shi damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar nan a karo na uku ba.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a taron kwamitin zartarwa wadda jam’iyyarsa ta APC ta gudanar a birnin Abuja.
Maganar da shugaban kasar yayi ta sabawa rade radin da ake ta yi cewa shugaban kasar wanda wa’adin mulkin sa zai kare a shekarar 2023 na shirin canja tsarin mulkin Najeriya domin tsayawa takarar shugaban kasa a karo na uku.
Amma da yake yiwa jami’an jam’iyyar tasa jawabi shugaba Muhammadu Buhari yayi kira gare su da su zage dantse wajen nasarar jamiyyar ta APC ,inda yace abun kunya ne jam’iyyar ta APC ta ruguje bayan kamala wa’adin mulkin sa a shekarar 2023 .