Connect with us

Labarai

Zainab Kwankwaso ta bukaci kotu ta raba aurenta da Gwamna Abba Kabir

Published

on

Zainab Musa Kwankwaso, matar Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ta shigar da ƙarar neman raba aurenta da gwamnan a wata kotun Upper Area Court da ke Gudu, Abuja, inda ta kuma bayyana shirinta na mayar da sadakin aurensu.

 

Jaridar DAILY NIGERIAN ce ta rawaito hakan bisa wasu takardun kotu da ta ce ta samu, inda ta bayyana cewa takardar gayyatar kotun mai lamba CV/97/26 ta umarci gwamnan da ya gurfana a gabanta ranar 17 ga Nuwamban 2026.

 

Zainab, wadda ’yar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ce, ta auri Abba Kabir Yusuf ne a ranar 29 ga Yulin 2006, lokacin da yake aiki a matsayin hadimin mahaifinta.

Rahoton ya kuma bayyana cewa ma’auratan na da ’ya’ya shida. Sai dai har yanzu ba a samu bayanin hukuncin kotu kan ƙarar ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!