Labarai
Gwamna Zulum ya dakatar da sakataren Karamar Hukumar Dikwa da wasu daraktoci

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya bayar da umarnin dakatar da sakataren ƙaramar hukumar Dikwa da wasu daraktoci bisa zargin rashin zuwa bakin aiki da sakaci wajen gudanar da ayyukansu.
Gwamnan ya bayar da umarnin ne a ranar Juma’a yayin ziyarar aiki da ya kai ƙaramar hukumar, inda ya tarar da wasu manyan jami’an ƙaramar hukumar ba sa wuraren aikinsu. Ya umarce su da su miƙa ragamar ayyukansu ga mataimakansu nan take, sai dai Daraktan Kula da Lafiya a Matakin Farko da Sakataren Ilimi ba su cikin waɗanda aka dakatar saboda suna bakin aiki a lokacin ziyarar.
Zulum ya kuma umarci Hukumar Kula da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomi ta Jihar Borno da ta tattara sunayen jami’an da abin ya shafa tare da fara matakan gudanarwa na cike guraben da suka bari, domin kada ayyukan ƙaramar hukumar su tsaya.
A yayin ziyarar, gwamnan ya kuma dakatar da aikin gina gidajen zama na ma’aikatan jinya a Babban Asibitin Dikwa, bayan ya nuna rashin gamsuwa da ingancin aikin. Ya ce za a dakatar da aikin har sai an samar da wani ɗan kwangila, yana mai gargaɗin cewa za a ɗauki mataki kan ’yan kwangilar da suka kasa bin ƙa’idojin da aka amince da su.
You must be logged in to post a comment Login