Connect with us

Labarai

Jami’an tsaron daji guda 1,008 sun kammala karbar horo a Katsina

Published

on

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya jagoranci bikin faretin kammala horon jami’an tsaron daji 1,008, ciki har da mata 18, waɗanda aka horas domin taimakawa wajen yaƙi da matsalar tsaro a jihar.

 

Gwamna Radda ya bayyana cewa ɗaukar jami’an ya biyo bayan ƙoƙarin da ya yi na neman tallafin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, bayan tabarbarewar tsaro a yankunan Musawa da Matazu. Ya ce shugaban ƙasar ya amsa buƙatarsa ta hanyar ƙarfafa ayyukan soji da ɗaukar sama da jami’an tsaron daji dubu ɗaya.

 

Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta samar wa jami’an kayan aikin da suke buƙata tare da ƙarfafa haɗin gwiwarsu da sauran hukumomin tsaro, musamman Katsina Community Watch Corps.

 

Ya kuma ce ana samun sauƙin matsalar tsaro, inda kasuwanni ke buɗewa, makarantu ke komawa aiki, manoma ke komawa gonakinsu, kuma a halin yanzu babu wata hanya a jihar da aka rufe saboda rashin tsaro.

 

Gwamnan ya gode wa Shugaba Tinubu da hukumomin tsaro, musamman Ofishin Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (ONSA), bisa gudunmawarsu. Ya kuma buƙaci sabbin jami’an da su kasance masu ladabi, ƙwarewa, biyayya da mutunta haƙƙin bil’adama yayin gudanar da ayyukansu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!