Kiwon Lafiya
Zamfara:Gwamnatin tarayya ta ja hankalin sarakunan gargajiya da al’ummar hana yan ta’ada mafaka
Gwamnatin tarayya ta gargadin masu rike da sarautar gargajiya a jihar Zamfara da sauran al’ummar jihar da kada su bawa ‘yan ta’addar yankin mafaka, kasancewar hakan zai kawo koma baya ga aikin jami’an tsaro na dakile ayyukan su a jihar.
Ministan tsaron kasar nan Mansur Dan-Ali ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, inda yace bayanan sirrin sun nuna cewa akwai wasu daga cikin manyan masu rike da sarautun gargajiya da ake zargin su da hannu a kashe-kashen da ke aukuwa a arewacin kasar nan.
Ministan tsaron ya kuma zargin wasu daga cikin dai-daikun mutane da hannu wajen bayar da bayanan sirri ga ‘yan ta’addar wajen gudanar da ayyukan su na tayar da hankulan jama’a, da kuma yiwa aikin jami’an tsaro karan tsaye wanda hakan na daga cikin kalubalen da ke addabar yadda za’a magance matsalar tsaron.
Mansur Dan-Ali ya kuma gargadin jama’a da ma kungiyoyi masu zaman kansu, musamman wadanda ke bawa bata garin mafaka da su kuka da kan su, tare da cewa duk wanda aka kama da hannu wajen kasha-kashen da ke faruwa ba wai a arewacin Najeriya ba kadai, shakka babu zai fuskanci fushin hukuma.
A cewar sa tuni aka bawa dakarun soji umarnin daukar tsauraran matakai kan duk wanda aka kama yana da hannu wajen taimakawa ‘yan ta’addar aiwatar da manufofin su na kasha-kashen mutanen da basu ji ba basu gani ba.