Labarai
Zamu cigaba da ayyukan alheri -TAYODA
Kungiyar cigaban matasa da hadin kai da Unguwar Tarauni TAYODA ta ci alwashin cigaba da gudanar da ayyukan alheri musamman wajen fatattakar matsalar shan miyagun kwayoyi da kuma samar da ingantaccen Ilimi a tsakanin matasan Tarauni.
Shugaban Kungiyar Abba Sagir Isahaq ne ya bayyana hakan lokacin taron shekara-shekara da kungiyar ta saba gudanarwa mai taken “Makon Tayoda” domin wayar da kan matasa wajen kaucewa aikata miyagun dabi’u.
Abba Sagir ya kara da cewa suna hada wasu daga cikin makarantun gwamnati da masu zaman kansu har ma da makarantun Islamiyyu wajen shirya musu gasa a tsakanin su domin bunkasa harkar Ilimin su domin ciyar dasu gaba.
Kungiyar Rumbun abinci na taimakawa yara masu tamowa da abincin gina jiki a Kano
Kungiyar GREKIN ta nemi gwamnatoci da su inganta tituna
‘Yan Najeriya na fuskantar karancin abinci – kungiyar FAO
Da yake nasa Jawabin Sakataren Kungiyar ta Tayoda Inuwa Yusuf Tarauni kira ya yi ga iyaye dasu tashi tsaye wajen ciyar da harkokin ilimin ‘ya’yan su tare kuma da neman gudunmawar iyaye wajen tallafawa harkokin kungiyar.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa kungiyar ta Tayoda na kara kira ga sauran al’ummar karamar hukumar Tarauni baki daya dasu cigaba da baiwa kungiyar hadin kai domin ciyar da harkokin Ilimi gaba.