Labarai
Kungiyar GREKIN ta nemi gwamnatoci da su inganta tituna
Shugaban kungiyar Greater Kano Initiative GREKIN Kwamared Kabiru Marmara yayi kira ga gwamnatin tarayya da sauran Gwamnatocin jihohin kasar nan dasu kawo karshen lalacewar manyan titunan kasar nan sakamakon munanan hadduran da titunan ke haifarwa a Najeria.
Kabiru Marmara ya ya bayyana hakan ne lokacin gudanar da tattakin da kungiyar ta gudanar domin tunawa da ranar wadanda suka gamu da matsalar hadari a duniya da majalisar dinkin duniya ta ware kowacce ranar sha bakwai ga watan Nuwaban kowacce shekara domin tunawa dasu.
Kwamared Kabiru Marmara ya kara da cewa kawo karshen lalacewar manyan titunan kasar nan ne kadai zai rage yawan mace – macen dubban mutane da Najeria ke fama dashi , a don haka ne yace yana kira ga gwamnatoci suyi gaggawar kawo karshen wannan gagarumar matsala domin rage yawan mutuwar mutane.
‘Yan Najeriya na fuskantar karancin abinci – kungiyar FAO
Rundunar sojan sama ta lalata maboyar kungiyar ISWAP
Kungiyar kishin al’ummar Kano za ta gina cibiyar fasaha
Shugaban Kungiyar ya nanata cewa sakamakon binciken da suka gudanar a Hukumar kashe gobara ta Kano da kuma sauran Chaji offisoshin ‘yan sanda na Kano sun gano suna fuskantar matsalar karancin jini wanda hakan yasa kungiyar zata fara ba yarda jini kyauta ga wadannan hukumomi domin tallafawa rayuwar su.
Wakilin mu Abdulkarim Muhammad Abdulkarim Tukuntawa ya ruwaito cewa kungiyoyi masu zaman kansu da sauran jami’an tsaro da dama ne suka halarci tattakin domin wayarwa da mutane kai don tallafawa wadanda suka gamu da matsalar Haddura iri daban – daban a fadin kasar nan.