Labarai
Zamu ciyo bashi domin cike giɓin kasafin shekarar 2022- Ministar Ƙudi
Gwamnatin tarayya na shirin karɓo bashin Naira tiriliyan 4 da biliyan tamanin da tara daga cikin gida da waje don cike giɓin kasafin kuɗinta na shekara 2022 da ya kai sama da Naira tiriliyan sha uku da biliyan casa’in da takwas sakamakon rashin samun kuɗaɗen shiga.
Ministar kuɗi kasafi da tsare-tsaren Hajiya Zainab Ahmad ce ta bayyana hakan a Abuja, a wani taron tattaunawa da kwamitin majalisar wakilai kan sha’anin kuɗi.
Zainab Ahmad ta ce, faɗuwar darajar naira da sauye -sauyen da babban bankin Najeriya ya yi a baya -bayan nan ya ƙara dagula harkokin samun kuɗi a Najeriya.
A cewar ta matakin matsin lamba kan kasuwar canjin kuɗaɗen waje ya taka rawa, har ma ta ce har yanzu masu zuba jari ba su dawo kasuwar hada hadar canji a Najeriya ba.
You must be logged in to post a comment Login