Labaran Kano
Zamu dau matakan kare hakkin ma’aikata -Hadakar kungiyar masana’antu
Gamayyar Kungiyoyin Masana’antu masu zaman Kansu , sun Kalubalanci gwamnatin tarayya da ta jiha da su dau matakin da ya dace wajen kare hakkin ma’aikata tare da tabbatar da hakkokin su bisa adalci da doka kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar nan ya basu.
Babban Sakatare na kungiyar Teloli , Masaku da masana’antu na kasa Kwamred Ali Baba, ne yayi kiran , a wani taron manema labarai da ya gudana a ofishin su, don sanar da matsayar su dangane da cin zarafin ma’aikata.
Labarai masu alaka.
Ministan kwadago ya sha alwashin fara aiwatar da tsarin mafi karancin albashi
Kungiyar kwadago ta bukaci a dau matakan Kariya na Corona
Kwamred Ali Baba, ya koka kan cin zarafin ma’aikata da wani Kamfanin Shinkafa yayi na kulle wasu ma’aikatan sa tare da tursasa musu wajen yin aiki mai kama da bauta , wanda hakan ya ce ya saba karara da ‘yan cin ma’aikatan.
Ali Baba, yace zuwa yanzu haka sun bada wa’adin mako daya ga Babban Daraktan Ma’aikatar aiyyuka ta Kasa mai lura da shiyyar Kano , da ya kalubalanci al’amarin tare da yin Allah wadai wanda sabawar hakan zasu dau matakin da ya dace da doka ta basu dama.
Haka zalika hadakar kungiyar ta sha alwashin yin Zanga -Zangar Lumana , tare da Kalubalantar Gwamnatin tarayya da ta jiha bisa matakan da suka dace matukar sun nuna halin ko in kula da hakan.
You must be logged in to post a comment Login