Labarai
Zamu fara sayar da gidajen da ba’a biya musu kudin kasa – El-rufai
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmed El-Rufai ya ce, suna gab da fara sayar da gidajen da al’umm suka mallaka wanda basa biyan kudin kasa.
Gwamna El-Rufai ya bayyana hakan ne a zantawar sa kai tsaye da kafafen yada labaran jihar a ranar Alhamis.
El-Rufai ya ce, akwai alumma da dama dake son zama a jahar Kaduna, a don haka nan bada jimawa ba gwamnati zata fara kwace gidajen da ba’a biya musu kudin kasa don ta bai wa masu son zama a jihar damar mallaka.
Gwamnan ya kara da cewa, duk wanda ya mallaki gida a jihar akwai kudin da ya kamata ya dinga biya na kasa duk karshen shekara, amma da yawan su basa biya, a don haka nema ya ce, gwamnati ta tattara bayanan al’ummar dake zaune a gidaje ba bisa ka’ida ba, kuma nan bada jimawa ba gwamnati zata kwace gidajen.
Malam Nasiru ya ce, wasu daga cikin su ba iya kwace gidan kawai za ayi ba “zamu mika su hannun jami’an tsaro kan karya dokar da suka yi na kin biyan gwamnati hakkin ta”.
Gwamnan ya kuma yi kira ga al’umma da su tabbatar sun yi takardar mallakan muhallin da suke ciki don gudun kar aiki ya biyo ta kan gidan da kake ciki a madadin a biya ka diyya sai a koma ana tuhumar ka.
A karshe ya shawarci al’umma da su tabbatar sun yi takardun mallakan fili a fadin jahar, “hukumar da alhakin mallakar fili ya rataya a wuyan ta, na yawo unguwa-unguwa don yiwa al’umma takardar mallakan fili a cikin sauki”.
You must be logged in to post a comment Login