Labarai
Zamu fito da sabbin dabaru na yaki da cutar lassa- Ministan lafiya
Gwamnatin tarayya ta yi alkawarin fito da sabbin dabaru na yaki tare da shawo kan cutar zazzabin Lassa, ta hanyar bude dakunan gwaje-gwaje wato Laboratory, da samar da isassun magunguna da ka iya dakile cutar cikin kankanin tOkaci.
Ministan Lafiya Mista Osagie Ehanire ne ya bayyana haka a yau a taron hasu
Kano 2020 Primary Heafthcare summit, da aka gudanar a babban dakin talro ruwa da tsaki na harkokin lafiya na jihar Kano tun daga tushe, mal taken na Coronation Hal dake fadar gwamnatin jihar Kano.
IiStd Usagie Emmanuel Ehanire ya kara da cewa a kokarin da gwamnatin tarayya ke yi na ganin cewar an bunkasa harkokin kiwon lafiya a kasa baki daya, a shiye take ta hada hannu da ko wace gwamnati tun daga matakin Jtha har zuwa na kananan hukumomi, musamman wajen ba da tallafi na kayan aiki da kudade da shawarwarl don ganin an samar da al’umma mai lariya a Tadin kasa.
Da yake na sa jawabin gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ce a kokarin da gwamnatinsa ke yi na inganta fannin kiwon lafiya a jiha, ta
ware kudi sama da naira billyan biyu don inganta asibitocin da ke sabbin masarautu guda hudu don samar da had aid 400 a cikinsu, wanda hakan zai kara kusanta aľ’ummar karkara tare da samar musu kayan kiwon lafiya a mataki na farko.
Wakilinmu na fadar gwamnatin jihar kano Aminu Halilu Tudunwada, ya rawaito mana cewa kungiyoyin duniya dake ba da tallafi a bagaren harkOkin
lafilya da suka hada da DFID, USAID, WHO da UNICEF, sun halarci taron tare da alkawarin tallafawa gwamnatin jiha wajen bunkasa harkokin lafiya.