Kasuwanci
Zamu fito da sabbin hanyoyin bunkasa kasuwanci a Kano-ICAN
Kungiyar kwararrun akantocin Nijeriya reshen Jihar Kano wato ICAN ta bayyana cewa ‘wasu daga cikin manyan muradun data sanya a gaba shine fito da tsari na musamman da zai habaka kasuwancin jihar Kano, da zai taimaka musu wajen yin gasa da kasuwannin duniya’.
Sabon Shugaban kungiyar Malam Habibu Ayuba ne ya bayyana hakan yayin bikin rantsar dashi, dama sauran sabbin jagororin kungiyar daya gudana a jiya Asabar.
Malam Habibu Ayuba ya Kuma ce ‘za Kuma su samar da kyakyawar alaka tsakaninsu da makarantun Jihar Kano, don bunkasar iliminsu, da zai taimaka wajen samar da kwararrun akantocin a Jihar’.
A hannu guda Kuma ‘zasuyi tafiya kafada-da -kafada da gwamnatin Jihar, don bunkasar al’amuran kasuwanci a jihar’.
Shugabannin Kungiyar da aka rantsar a Karo na 42, sun tabbatar da cewa ‘zasuyi duk Mai yiwuwar wajen samarwa Kungiyar, dama Jihar Kano cigaba Mai dorewa’.
You must be logged in to post a comment Login