Labarai
Zamu gina shaguna don cigaban Dakata -Lamin Sani Kawaji
Shugaban karamar hukumar Nassarawa Alhaji Lamin Sani, yace karamar hukumar zata cigaba da aikin data dauko na gina shaguna a layin Sarauniya dake unguwar Dakata.
Hakan ya biyo bayan dambarwar zargin karamar hukumar da yin aikin ba bisa ka’ida ba, wanda al’ummar yankin da dama suka nuna adawar su da yin aikin kasancewar zai gurbata muhallin su duba da yadda tsarin ginin zai tsuke layin da ta’azzara matsalar data addabi layin shekara da shekaru na magudanar Ruwa.
Alhaji Lamin Sani, ya bayyana haka ne a ofishin sa, a lokacin daya ke zantawa da wakilan jama’ar unguwar da suka kai kukan su tare da korafin aikin don nemo bakin zaren aikin.
Labarai masu alaka.
Al’ummar Dakata sun koka akan ginin shaguna bisa magudanar ruwa
An dakatar da gasar Firimiyar kasar Ingila sabo da-Corona
Lamin Sani,ya ce hukuma nada hurumin yin aiyyukan da ta ke so, na cigaba da bunkasa yankuna ,kasancewar ita take da iko da duk wasu filaye dake karkashin ikonta, ko jama’a na so ko akasin haka matukar aikin bai saba ka’ida ba, kuma zai amfani al’ummar yankin da kawo musu cigaba.
Al’umma da dama na unguwar sun soki lamarin tare da barranta kansu da wakilcin wanda suka zauna da shugaban karamar hukumar, da ayyana cewar ba da yawun su ba.
inda suka kara dacewa in har hukumar ta dau niyyar yin aiki na bunkasa yankin, sun fi bukatar gina musu Islamiyya a wajen da ake takaddama ba wai ginin shaguna ba.
Haka zalika, jama’ar yankin sun sha alwashin bin hanyoyin da suka dace don ganin cewar ba ayi amfani da karfin mulki ba ,wajen shiga hakkin su da yancin su ta hanyar yin ginin , a matsayin su na ‘yan kasa masu ‘yanci.
You must be logged in to post a comment Login