Labarai
Zamu hukunta masu cunkuson jama’a-FRSC
Hukumar kiyaye abkuwar hadurra ta kasa FRSC, za ta fara kama masu cun kusa jama’a a ababen hawa.
Hukumar kiyaye abkuwar hadurra ta kasa (FRSC), ta ce za ta fara daukan tsauraran matakai kan masu ababen hawa da ke yin lodin wuce kima.
Mai magana da yawun hukumar a nan Kano, Kabiru Ibrahim Daura ne ya bayyana haka yayin zantawa da tashar freedom rediyo.
Kabiru Ibrahim Daura, ya ce, daukar matakin ya zama wajibi domin dakile yaduwar cutar Corona wacce ta ke da saurin yaduwa a cikin al’umma ta hanayar yaduwa.
Labarai masu alaka.
Takai:Mutane 19 ne suka rasa rayukansu a wani hatsari da ya afku a kauyen Dinyar Madiga
Ganduje : za’a rufe kan iyakokin jihar Kano COVID-19
“Ko da masu baburan hawa ba a amince su dauki sama da Mutum biyu ba, ma’ana da mai tuka babur din da Kuma Mutum daya” inji Kabiru Ibrahim Daura’’.
Ya ce tun farko dama yin lodin wuce kima laifi ne, saboda haka hukumar za ta kara sanya ido kan lamarin domin kare lafiyar al’ummar jihar Kano dama kasa baki daya.
Wakilin mu Abdullahi Isa, ya ce hukumar ta sha alwashin yin duk mai yiwuwa wajen ganin an samu takaitar zirga zirga don dakile barzanar yaduwar cutar.
You must be logged in to post a comment Login