Labarai
Zamu inganta noman kayan lambu Sasakawa
Kungiyar nan da ke rajin kawo ci gaba akan harkokin noma a Afrika wato SASAKAWA da kuma hadin gwiwar Bankin Muslunchi tace samar da sabbin dabarun noman kayan lambu hanya ce da za ta habaka tattalin arzikin jihar Kano.
Shugaban kungiyar na Kano Abdulrashid Hamisu Kofar Mata ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da kungiyar ta fitar.
Kofar Mata ya ce, a yanzu haka sun horas da manoma dabarun noman rani, kuma za su ci gaba da bada horon ga manoma, domin samun yabanya mai yawa.
Ya ƙara da cewa kungiyar na ci gaba da bincike kan samarwa manoma iraruwa masu kyawu da inganci.
You must be logged in to post a comment Login