Labarai
Zamu inganta wuraren bude ido da muke dasu a jihar Kano – Lajawa
Hukumar kula da masu yawon bude ido ta jihar Kano ya ce nan ba da dadewa ba za su dawo da martabar wuraren da ake jima da rini a fadin jihar Kano.
Alhaji Yusuf Ibrahim Lajawa ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.
Ya ce babbar nasarar da su ka samu ita ce sabunta dokar da tayi dai dai da zamani domin suyi dai dai da yadda duk wani bako zai bi dokar ba tare da kawowa addini ko al’ada ba.
Lajawa ya ce”nan ba da dadewa ba gwamnatin jihar Kano za ta gyara kasuwar dukkan abubuwan gargajiya da kuma na tarihi wadanda su ke cikin kasuwar kurmi.
You must be logged in to post a comment Login