Labarai
Zamu kawowa Kano cigaba a ɓangaren yanka filaye
Samar da wakilai a dukkanin shiyoyi zai taimaka wajen gudanar da jagoranci cikin nasara da kawo cigaba a jihar kano
Sarkin fawan Kano Alh Isiyaku Alin Muli ne ya bayyana haka alokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen bikin nadin wakilai da Sarkin Dillalan kano yayi a Fadarsa dake kofar ruwa karamar hukumar Dala
Sarkin fawan yace nadin da sarkin dillalan yayi na wadan da zasu taimaka masa don gudanar da ayyukansa cikin sauki zai taimaka kwarai wajen dakile shigowar bata gari cikin jihar kano
Da yake nasa Jawabin Sarkin Dillalan Jihar Kano Alh Mustapha Abdullahi Arrow yace wannan nadin da Yayi zai taimaka masa kwarai wajen gyara harkar dillanci da bada hayar gidaje a jihar kano.
Ya kuma ja hankalin wadan da suka rabauta da wadannan mukamai dasu ji tsoron Allah wajen gudanar da aikinsu
Da yake jawabi jim kaɗan bayan naɗa shi a matsayin makaman sarkin Dillalan jihar Kano Alhaji Naziru Tijjani ya ce zasu kasance masu mayar da hankali wajen kawowa wannan ƙungiya ta su ci gaba a dukkan ɓangarori.
Haka kuma wannan naɗin da akayi musu an ƙara musu ƙaimi wajen gudanar da aikin su da samarwa da jihar kano ci gaba a ɓangaren su na dillanci.
Daga ƙarshe sarkin Dillalan Kano ya godewa gwamnatin Jihar kano da ayyukan da take gudanarwa a jihar ya kuma jinjinawa masarautar kano bisa jagorancin Sarkin kano Alh Aminu Ado Bayero da irin karfafa musu gwiwa da kuma basu shawara da take wajen gudanar da ayyukan su.
You must be logged in to post a comment Login