Labarai
BAZOUM: Za mu nuna wa Duniya ba iya Uranium kaɗai muke da ba
Jamhuriyyar Nijar na shirye-shiryen karɓar baƙuncin wani babban taron shugabannin ƙungiyar ECOWAS kan ma’adanai.
Taron dai zai fara tun daga ranar 1 zuwa 3 ga watan Disambar wannan shekarar, a babban birnin Yamai, wanda zai haɗa shuwagabannin ƙasashe goma sha biyar na ECOWAS, kuma zai bawa ƙasar ta Nijar damar bayyana albarkatun ƙasar ta.
Yanzu haka dai tuni aka ƙaddamar da kwamitin kula da shirya wannan babban taro, ƙarƙashin ministan man fetur na ƙasar Sani Issofou Muhammad.
Madam Fatomatou, mataimakiyar magatakardar ofishin ma’aikatar ministan ma’adanan ƙasa, kuma ƴar kwamitin ta bayyana cewa “wannan babbar dama ce ga ƙasar Nijar inda za tayi bajakolin ma’adanan ta, wanda ka iya jawo wasu ƙasashen su shigo cikin ta domin zuba hannun jari”
Ƙasar Nijar dai tana da tarun ma’adanai iri-iri, wanda ya hada da Uranium, da Zinare, da Iskar Gas, da ƙarafuna, da gawayi, da kuma man fetir.
You must be logged in to post a comment Login