Labarai
Zamu tara Naira miliyan dubu shida a badi -KAROTA
Hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA ta bayyana cewa za ta tara wa gwamnatin jihar Kano Naira miliyan dubu shida a shekara mai kamawa.
Shugaban hukumar Baffa Babba Danagundi ne ya bayyana hakan a jiya Litinin yayin da yake tattaunawa da manema labarai a shalkwatar hukumar.
Shugaban hukumar ta KAROTA ya kuma ce, za su samar da kudaden ne ta hanyar kudin tarar da za a karba daga masu ababen hawan da suka karya doka jami’an hukumar suka cafke su.
Haraji: Mun rage Adaidaita Sahu zuwa dubu dari- KAROTA
An cafke direban da ake zargin yayi sanadin mutuwar jami’in KAROTA
An cafke direban da ake zargin yayi sanadin mutuwar jami’in KAROTA
Haka kuma ya kara da cewa, yanzu haka hukumar ta sanya jami’anta na yin aiki na tsawon sa’o’i 24, inda hakan ya basu damar kame tarin masu manyan motoci wadanda ke tafiya cikin dare amma ba su da fitila wand hakan ke yawan haifar da aukuwar hadurra.
Baffa Babba Danagundi, ya ce an samu raguwar matsaloli tsakanin jami’ansu da direbobi, inda ya ce a bana jami’ansu 2 ne suka mutu yayinda mutane 35 suka samu raunuka sakamakon kade su da masu ababen hawa suka yi.