Labarai
Zan kara bai wa mata fifiko a gwamnati na – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kara jaddada matsayin gwamnatinsa na ci gaba da kyautata rayuwar ‘ya’ya mata a Nigeria.
A cewar shugaba Buhari tuni ya umarci ma’aikatar kula da harkokin mata da takwararta ta shari’a, da su yi aiki tare da majalisun dokokin tarayya wajen samar da dokoki da za su bunkasa rayuwar mata.
Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne a jiya juma’a, lokacin da ya ke ganawa da wata tawagar kungiyoyin mata ta duniya a fadar asorok.
‘‘Buri na shine ganin ‘ya’ya mata sun samu gurabe masu yawa a harkokin gudanarwa, wanda hakan zai faru ne kawai idan aka yi kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar nan’’ a cewar shugaba Buhari.
Shugaban kasar ya kuma jinjinawa Amina Muhammed, mataimakiyar sakatare janar na majalisar dinkin duniya, Ngozi Okonjo Iweala shugabar cibiyar kasuwanci ta duniya da kuma Fatima Muhammed Kyari, wadda ta kasance wakiliyar kungiyar kasashen afurka ta (AU) a majalisar dinkin duniya.
You must be logged in to post a comment Login