Labarai
Zan kawo sabbin tsare-tsaren ci gaba a fannin Ilimi, Noma da Lafiya idan ya zama Sanata- Gawuna

Dan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya a Jam’iyyar NDC kana tsohon dan takarar Gwamnan Kano na Jam’iyyar APC a shekarar 2023, Alhaji Nasir Yusuf Gawuna, ya sha alwashin samar da sabbin tsare -tsaren ci gaba a fannin Ilimi, Noma da Lafiya ga al’ummar da zarar ya samu nasara a zabe mai zuwa.
Gawuna ya bayyana hakan ne ya yin ganawa da ‘yan Jaridu kan manufofin sa da yake da su, kuma zai aiwatar don ci gaban al’umma.
Nasiru Gawuna, wanda shugaban kwamitin yakin Neman zaben sa Dr Saleh Adamu Kwaru , ya yi jawabi a madadin sa ya ce lokaci ya yi da za a sauya tsarin siyasar wakiltar al’umma da zata amfanar dasu kai tsaye.
Nasiru Yusuf Gawuna , ya kuma bukaci Dumbin magoya baya da sauran ‘yan siyasa da su gudanar da gangamin Neman zabe ba tare da cin mutuncin juna ba da tashe -tashen hankula.
You must be logged in to post a comment Login