Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta rufe makarantar Prime College na tsawon mako 2

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta rufe makarantar Prime College dake nan Kano, na tsawon sati biyu sakamakon karya wasu dokoki da ci gaba da gudanar harkokin sha’anin karatu da aiki ba bisa ƙa’ida ba. 

 

Shugaban hukumar Kula da Makarantu Masu zaman kansu da na sa-kai ta Jihar Kano, wato Kano State Private and Voluntary Institute Board Kwamred Baba Abubakar Umar, ne ya bayyana hakan ya yin wata ganawa da manema labarai a nan Kano.

 

Baba Abubakar Umar, ya ce makarantar ta yi watsi da takardar da hukumar ta tura mata har sau biyu na binka’idojin da suka dace na sabunta lasisin aiki kan doka, sai dai har kawo yanzu basu ji da ga hukumar makarantar ba.

                                                        

Kwamred Baba Abubakar Umar, ya ce, hukumar ba ta da nufin rufe ko dakatar da kowacce makaranta ko dakatar da karatun dalibai, sai da ba zata lamunci karya dokoki ba ko yin katsalandan a duk abinda zai kawo koma baya da ci gaba ilimin matasa da jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!