Labarai
Zan rantse da Qur’ani ban yi zambar kudi ba-Shehu Sani
Tsohon Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya ki amincewa ayi amfani da na’urar gwaji da ke gano mutanen da su ka yi karya kan wani batu da ake zarginsu wato Lies Detective Machine.
Idan za a iya tunawa Sanata Shehu Sani ya na hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC tun a shekarar da ta gabata sakamakon zargin sa da zambatar wani dan kasuwa kuma shugaban kamfanin ASD Motors Alhaji Sani Dauda da nufin bai wa shugaban hukumar EFCC Ibrahim Magu don kamun kafa.
Shehu Sani:Muna karbar naira miliyan goma sha uku da dubu dari biyar a kowanne wata
PRP zata daukaka kara kan hukuncin kotu ta yanke na sanata Uba Sani na jami’yyar APC
EfCC dai ta zargi Sanata Shehu Sani da karbar kudin da ya kai dala dubu Ashirin a hannun dan kasuwar.
Jaridar ‘THE NATION’ ta ruwaito cewa an ji Sanata Shehu Sani a jiya Litinin yana cewa sam shi kam ba zai yadda ayi amfani da wata na’ura akan shi don gano yana da gaskiya ko akasin haka ba, domin kuwa bai amince da na’urar ba, maimakon haka ya gwammace ya rantse da Alqur’ani