Labarai
Zanga-zanga ta tilasta rufe gidan talabijin din kasar Mali
Masu zanga-zanga a Mali sun tilasta wa kafar yaɗa labaran ƙasar katse shirye-shiryenta yayin wani gagarumin jerin gwano a Bamako, babban birnin ƙasar.
‘Yan sanda sun hah-harba bindiga kuma sun yi amfani da hayaƙi mai sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zanga a dai-dai lokacin da wasunsu ke ƙoƙarin kutsawa cikin ginin majalisar dokokin ƙasar.
Wannan ce zanga-zanga karo na uku cikin wata guda da ake gudanarwa a kasar don neman Shugaba Ibrahim Boubakar Keita ya sauka daga kan mulki.
Cikin koke-konen al’ummar kasar akwai rashin gamsuwa kan yadda ake tunkarar rikicin masu iƙirarin jihadi da ya shafe tsawon lokaci, da matsalolin tattalin arziƙi da kuma taƙaddama game da zaɓukan ‘yan majalisa.
You must be logged in to post a comment Login