Labarai
Ziyarar da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kawo a Kano
Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya kawo ziyarar aiki jihar Kano a ranar Alhamis ɗin nan.
Ziyarar ta shugaba Buhari ta ƙunshi ƙaddamar da aikin layin dogo daga Kano zuwa jihar Kaduna, da kuma Lagos zuwa Kano.
Buhari, ya sauka a filin taron da aka shirya gudanarwa a Zawaciki da ke ƙaramar hukumar Kumbotso, daura da tashar Tsandauri ta Ruwa ta Dala Inland Dry Port.
Da yake jawabi yayin ƙaddamarwar shugaba Buhari, ya ce aikin na daga cikin ƙudurorin gwamnatin sa na farfadowa tare da cike giɓin da ake da shi na harkar sufurin jirgin ƙasa a fadin ƙasar nan.
A cewar shugaban Layin-Dogon, zai taimaka wajen harkokin kasuwanci tsakanin jihohin kudancin ƙasar nan da Arewaci, musamman ma cibiyoyin kasuwancin wato Kano da Lagos.
Haka zalika shugaba Buhari, ya ce aikin da zarar an kammala shi zai taimaka wajen rage yawan fasinjojin da suke amfani da motoci don yin zirga-zirga tsakanin jihohi, kasancewar zai haɗe, jihohin Lagos, Ogun, Osun Kogi ,Niger, Abuja da kuma Kaduna, har zuwa jamhuriyar Nijar.
You must be logged in to post a comment Login