Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ƴan sanda sun cafke jami’in da ya hare ɗan kasuwa a Abuja

Published

on

Rundunar ‘ƴan sandan birnin tarayya Abuja, ta ce, ta cafke wani jami’in gidan gyaran hali da ake zargi da harbe wani mutum mai suna Ibrahim Yahaya a kasuwar Wuse da ke tsakiyar birnin.

Kisan mutumin dai ya janyo hatsaniya a kasuwar da yammacin jiya Talata, lamarin da ya janwo asarar dukiya.

Hakan na ƙunshe ne ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ta Abuja, Josephine Adeh ta fitar, ta ce jami’in ya harbe Yahaya ne a lokacin da yake yunƙurin tserewa bayan da rundunar tsaftace Abuja ta kama shi ta kuma gurfanar da shi a gaban kotun tafi da gidanka da ke Kasuwar Wuse, inda aka yanke masa hukunci.

Sanarwar ta ƙara da cewa yanzu haka rundunar ta na tsare da jami’in inda take gudanar da bincike.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!