Labarai
Ƙudurin dokar kasafin kuɗin baɗi ya tsallake karatu na biyu
Ƙudurin dokar kasafin kuɗin baɗi, da gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ya gabatar, ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dokokin jihar Kano.
Ƙudurin ya kai wannan mataki ne bayan da mambobin majalisar suka amince da karatun na biyu wanda shugaban masu rinjaye na zauren Alhaji Lawan Hussaini Chediyar ƴan Gurasa ya gabatar yayin zaman majalisar na yau Litinin ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore.
Bayan amincewa da ƙaratun, majalisar ta kuma bai wa kwamitinta na harkokin kasafi tsawon makonni uku da ya gudanar da aikin kare kasafin ga ma’aikatu da hukumomin gwamnati tare da gabatar da rahoto.
Wannan dai na zuwa ne bayan da aka buɗe majalisar daga yajin aikin da ƙungiyar ma’aikatan majalisun jihohin ƙasar nan suka yi na fiye da makonni uku.
You must be logged in to post a comment Login