Connect with us

Labarai

Ƴan ƙasa da shekaru 13 sun fafata a gasar ƙwallon ƙafa da kamfanin Milo ya shirya a Kano

Published

on

Kamfanin Nestlé Milo tare da haɗin gwiwar tsohon Kyaftin din Ƙungiyar Ƙwallon Kafa ta Najeriya ta Super Eagles, Ahmed Musa, sun shirya gasar ƙwallon ƙafa ta yara ’yan ƙasa da shekaru 13 a Kano.

‎Kamfanin ya ce ya shirya gasar ce da nufin zakulo zaƙaƙuran yara masu baiwar ƙwallon ƙafa a faɗin arewacin Najeriya.

‎Ya ce maƙasudin shriya gasar ta kusan tsawon mako uku shi ne domin a horar da yaran sannan a koya musu muhimmancin jajircewa, sadaukarwa da kuma fito da baiwar da suke da ita.

‎Da yake jawabi a lokacin bude gasar, wakilin kamfanin na Milo, Gilbert Tweneboah-Koduah, ya ce shirya gasar wani ɓangare ne na kamfanin na ganin cewa an yi amfani da wasanni wajen bunƙasa hazaƙar yaran, ba wai a fannin karatu kawai ba.

‎Ya ce sama da ƙungiyoyi 16 ne suka fafata a gasar yayin da gogaggun masu horarwa suka kasance tare da su.

‎Gilbert ya kuma ce kodayake an fafata sannan an fitar da zakaru, amma babban burin gasar shi ne fito da yara masu hazaƙa daga cikin wadanda suka fafata a cikinta, yana mai cewa suna fatan ganin cewa gasar za ta zama ta shekara-shekara a nan gaba.

‎Shi ma Ahmed Musa, wanda kuma Jakadan kamfanin na Milo ne, ya ce an ƙirƙiri gasar ce domin farfaɗo da ƙwazon yara da kuma zaƙulo masu baiwa daga cikinsu, kwatankwacin irin damar da ya ce shi ma ya samu lokacin yana yaro.

‎Ya kuma ce an zabo yaran ne saboda a samu damar gano masu baiwa domin a horar da su, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa nan gaba za a samu zakarun da za su buga wa Najeriya wasa daga cikinsu.

‎A cewar Manajan filin wasan Ahmad Musa mai suna Musa Muhammad, an shirya gasar ce domin a jawo kananan yara a jika kasancewar akasarin gasar an fi shirya ta ne ga manya.

‎Ya ce “A kan haka ne kamfanin Milo ya ce mu nemo yara ’yan shekara takwas zuwa shekara 13 saboda su ma a karfafa musu gwiwa a nuna ana yi da su”.

‎Ya ce a sakamakon gasar, kulob din Khamis Boy ne suka zo na daya, sai BC Academy da suka zo ba biyu, sai Legacy da suka zo na uku, inda ya ce kowannensu sun samu kyaututtukan kudi masu yawa.

‎Ya kuma shawarci yaran da su dage da karatu sannan su haɗa shi da kwallon, yana mai cewa hakan zai ɗauke musu hankali daga abubuwa marasa kyau kamar shaye-shaye sannan ya sa su zama mutane na gari idan sun girma.

‎Shi ma Manajan kulob din Khamis Boy wanda suka zo na daya, ya ce sun samu tukwicin naira miliyan daya, sannan ya gode wa kamfanin na Milo saboda ba su damar shiga gasar a fafata da su har suka kai ga nasarar.

‎Shi ma Dayo Adetoya, Manajan kamfanin milo a shiyyar Arewa maso Yamma, ya ce an shirya gasar na a haɗaka tsakanin kamfanin da Ahmed Musa domin fito da hazaƙar yara a fagen kwallon kafa sannan a ba su damar ƙarfafa mafarkinsu na zama zakaru a nan gaba.

‎Ya ce, “A sakamakon wannan gasar da aka shirya, na ga yaran da suna da alamun zama haziƙan ’yan ƙwallo a nan gaba. Wannan ne karo na farko da ake yin wannan hadakar tsakanin kamfanin Milo da Ahmed Musa.

‎“Mun gano yara masu hazaka sosai kuma daga nan za mu ga hanyar da za mu bi domin ganin mun tallafa musu ta hanyar ba su horo har mafarkinsu ya kai ga tabbata saboda ganin cewa baiwarsu da ta bayyana a nan ba ta tafi a banza ba,” in ji Adetoya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!