Labarai
Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya ta yi watsi da ƙungiyar iyayen ɗaliban Unity Colleges

Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya, ta sanar da yin watsi da ƙungiyar iyayen ɗaliban Unity Colleges tare da cewa, ƙungiyar ba ta wakiltar ƙungiyoyin iyaye da malamai na makarantun guda 118 da ke faɗin ƙasa.
Hakan na cikin sanarwar da Daraktar Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta Ma’aikatar, Boriowo Folasade, ta fitar a jiya Litinin.
Sanarwar ta ce ƙungiyar ba ta da izinin yin magana a madadin makarantun Unity Colleges, ƙungiyoyin iyaye da malamai, iyaye ko masu kula da ɗalibai, saboda haka jama’a su yi watsi da duk wata sanarwa, umarni ko saƙon da ta fitar.
Ma’aikatar ta buƙaci iyaye da masu kula da ɗalibai su dogara da bayanan da take fitarwa da kuma na hukumomin makarantun da yaransu suke karatu, musamman kan abubuwan da suka shafi makarantu, ɗalibai da harkokin karatu.
Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya buƙaci iyaye su tabbatar da cewa yaransu sun koma makarantun su, kasancewar an fara zangon karatu na 2026/2027 a faɗin ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login