Connect with us

Labarai

Kwamitin da Gwamnatin Kano ta kafa mai yaƙi da kayan maye da Daba ya yi holin kayayyaki

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin gina sabuwar cibiyar killace matasan da aka kama da laifukan Tu’ammali da miyagun ƙwayoyi da kuma aikata ayyukan Daba da za a yi a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa.

Shugaban Kwamitin da Gwamnatin ta Kano ta kafa mai yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi da kuma ayyukan Daba Barista Muhyi Magaji Rimingado, ne ya bayyana hakan a a yau Talata yayin da ya ke yin holin nau’ikan kayan maye da kuma muggan makamai da su ka samu nasarar ƙwace wa.

Barista Muhyi, ya ce, dukkan wuraren da gwamnatin Kano ke da su na killace irin waɗannan matasa da ke Ƙiru ta cika sakamakon kame matasa fiye da 380 da suka yi.

Shugaban kwamitin ya ƙara da cewa, kwamitin ya samu wannan nasara ne yayin da ya cika watanni biyu da fara aiki.

Ya ƙara da cewa, tuni aka yanke wa matasa 230 hukunci cikin matasa 380 da su ka kama.

Muhyi Magaji Rimingado, ya kuma bayyana sunan tsohon shugaban ƙaramar hukumar Rogo Malam Yahuza Musa, wanda ya ce, yanzu haka ya na gaban kotu, inda ya ke fuskantar tuhuma bisa zarginsa da hannu a harkar kayan maye.

Haka kuma, ya bayyana cewa, mafi yawa daga cikin ƙwayoyin da su ka kama matasa na tu’ammali da su, duk magunguna ne na asibiti kuma ma su kyau, don haka sun fara shirin haɗa kai da hukumomi don tabbatar da ingancinsu tare da miƙa su ga asibitoci da nufin yin amfani da su ga marasa lafiya.

Muhyi, ya kuma nuna muggan makamai da wayoyin hannu da Dabur ɗin Adaidaita Sahu da Babu mai amfani da Lantarki da kuma wata mota wadda ke maƙare da miyagun kwayoyi wanda su ka samu nasarar kamawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!