Connect with us

Labarai

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da dattijan ƙauye a Maradun

Published

on

Ƴan bindiga sun yi garkuwa da dattijan wani ƙauye a ƙaramar hukumar Maradun da ke jihar Zamfara bayan sun yi yunƙurin yin sulhu sanadiyyar rashin tsaron da ke addabar yankin.

Lamarin ya faru ne a ƙauyen Magamin Diddi wanda rahotanni suka ce yana a kusa da ɗaya daga cikin dazukan da ƴan fashin daji ke da sansani.

A tattaunawarsa da BBC, shugaban ƙaramar hukumar Maradun Sunusi Ahmed Dosara ya tabbatar da faruwar lamarin, in da yace daga ƙididdigar da suka yi mutanen da ƴan fashin dajin suka riƙe “sun kai 39”.

Zamfara na cikin jihohin arewa maso yammacin Najeriya da suka daɗe suna fama da matsalar ƴanfashin daji masu kisa da kuma garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa.

Ayyukan ƴan bindigar sun durƙusar da harkokin tattalin arziƙi a yankin, musamman noma, wanda akasarin al’ummar yankin ke dogaro da shi.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!