Connect with us

Labarai

Sojoji sun ceto mutane 48 daga masu garkuwa a Kaura Namoda

Published

on

Dakarun Rundunar Operation Fansar Yamma sun ceto mutane 48 daga masu garkuwa a ƙauyen Magami da ke Karamar Hukumar Kaura Namoda a Jihar Zamfara.

 

Wannan na cikin sanarwar da Jami’in Yaɗa Labaran Rundunar, Laftanar Kanal Aliyu Danja, ya fitar a jiya Lahadi.

 

Sanarwar ta ce ‘yan ta’addan, wadanda suka shigo yankin da babura kusan 40, sun yi awon gaba da dimbin mazauna yankin da nufin garkuwa da su, kafin dakarun su isa wurin bayan samun kiran neman agaji.

 

Ya ce, sojojin sun yi artabu da ‘yan ta’addan, lamarin da ya tilasta musu sakin mutanen tare da tserewa cikin daji.

 

Rundunar ta ce, mutum 1 ya rasu yayin artabun, yayin da wasu 2 suka samu raunukan harbin bindiga kuma aka kai su babban asibitin Kaura Namoda.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!