Connect with us

Labarai

Gwamna Zulum ya ziyarci mutanen Ngoshe da aka kubutar daga hannun ‘yan ta’adda

Published

on

Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya ziyarci mutanen Ngoshe da aka kubutar daga hannun ‘yan ta’adda bayan sun shafe kusan watanni uku a tsare. A yayin ziyarar, ya sanar da cewa gwamnati ta fitar da miliyoyin nairori domin sake gina da farfado da al’ummar Ngoshe tare da tallafa wa wadanda abin ya shafa.

Wasu daga cikin wadanda aka kubutar sun bayyana irin wahalhalun da suka sha a lokacin da suke tsare, inda suka ce suna cin dawa sau daya kacal a rana. Sun kuma ce suna kwana a kasa da saman duwatsu, yayin da wasu daga cikinsu suka hadu da mutanen da suka shafe har watanni bakwai a hannun masu garkuwa da mutane.

Zulum ya yaba wa shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, da jami’an tsaro bisa kokarin da suka yi wajen ganin an kubutar da wadanda aka sace. Ya kuma ba da umarnin raba kayan agaji ga wadanda aka sako, tare da tabbatar da cewa gwamnati na aiki tare da sojoji domin samar da yanayin da zai ba mazauna Ngoshe damar komawa gidajensu cikin tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!