Labarai
Adeleke ya lashe kananan hukumomi 19 a zaben Gwamnan jihar

Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke na Jam’iyyar Accord, ya lashe zaben gwamna a kananan hukumomi 19 daga cikin 30 na jihar.
Babban abokin hamayyarsa, Bola Oyebamiji na Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), ya samu nasara a kananan hukumomi 11.
Sakamakon ya nuna cewa Adeleke ya samu gagarumar nasara a wasu daga cikin kananan hukumomin jihar, yayin da Oyebamiji ya yi nasara a sauran.
Daga cikin wuraren da Adeleke ya samu rinjaye akwai Ede ta Kudu, Ife ta Arewa, Osogbo da Ede ta Arewa, yayin da APC ta lashe Ilesa ta Gabas, Boripe, Irepodun da Obokun.
Haka kuma, APC ta samu kuri’u masu yawa a Irewole, Atakumosa ta Gabas, Ife ta Kudu, Ejigbo da Olorunda, inda ta samu nasara a wasu daga cikin wadannan kananan hukumomi.
Sai dai har yanzu ana jiran sanarwar karshe daga Hukumar Zabe ta Kasa, INEC, wadda ke kammala tattara tare da tabbatar da sakamakon zaben da aka gudanar ranar Asabar.
You must be logged in to post a comment Login