Labarai
Ɗan wasan Liverpool Diogo Jota ya rasu a hatsarin Mota

Ɗan wasan gaba na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool da kasar Portugal, Diogo José Teixeira da Silva, wanda aka fi sani da Diogo Jota, ya rasu a hatsarin mota yana da shekaru 28.
Haka zalika dan uwansa, Andre Silva, shi ma ya rasu a cikin hadarin, wanda ya faru a lardin Zamora na kasar Sifaniya.
Andre, mai shekaru 26, shi ma dan kwallon kafa ne a ƙungiyar Penafiel a gasar rukuni na biyu a Portugal.
A watan da ya gabata ne dai Jota ya auri masoyiyarsa da suka dade suna soyayya, Rute Cardoso, wadda suka haifi ‘ya’ya Uku tare.
Ya wallafa hotunan bikin a shafukan sada zumunta kwanan nan, baynda aka gudanar da bikin a ranar 22 ga Yuni.
Jota ya taimaka wa Liverpool wajen lashe gasar cin kofin Firimiyar kasar Ingila a kakar da ta gabata, kafin daga bisani ya taimaka wa Portugal lashe kofin Nations League a watan Yuni.
You must be logged in to post a comment Login