Labarai
Al’umma su dinga kai kara don kwato musu hakki-Majalisar dinkin duniya
Hukumar kare hakkin bil Adam ta kasa ta ce, kamata ya yi al’umma su riga kai kara inda ya kamata don kwato musu hakkin su.
Shugaban hukumar a nan Kano, Malam Shehu Abdullahi kiru ne ya bayyana hakan, a wani banagre na bikin ranar kare hakkin dan Adam ta duniya a yau Talata.
Malam Shehu Abdullahi na mai cewa, sanin hakki wajibi ga duk al’umma ta bangarori daban-daban don samun yancin su.
Lauya mai fafutukar kare hakkin bil adama ya rubuta wasika zuwa ga Shugaban kasa
Kungiyar Amnesty international ta ce sojojin kasar nan sunyi biris da gargadin boko haram
Wasu mazauna birnin Kano sun bayyana irin hakkokin su da aka danne musu wanda hukumomi ta kasa yin komai akai
Majalisar dinkin duniya ce dai ta ware duk ranar 10 ga watan Disanba kowacce shekara, a matsayin ranar kare hakkin bil Adam ta Duniya.
Wakilyar mu Aisha Muhammad Yalleman na da cikkaken rahotan a cikin labaran Duniya da kuma na muleka mu gano