Yayin da ake shirin fara Gasar Kofin Duniya ta FIFA ta 2026 da za a gudanar a ƙasashen Amurka, Canada da Mexico, idanuwan masu sha’awar ƙwallon ƙafa sun karkata ga manyan taurarin wasa da ƙasashen da ke daf da kafa sababbin tarihi. Rahotanni sun nuna cewa akalla tarihohi 20 ne za su iya karyewa a wannan gasa, musamman ta hannun fitattun ’yan wasa irin su Lionel Messi, Cristiano Ronaldo da Kylian Mbappe.
Kaftin din Argentina, Lionel Messi, na da damar ƙara yawan tarihin da ya riga ya mallaka a gasar Kofin Duniya. Messi, wanda ya buga wasanni 26 a gasar tare da zura ƙwallaye 13, na iya kusantar ko ma karya tarihin yawan ƙwallayen da ɗan wasan Jamus Miroslav Klose ya kafa da ƙwallaye 16. Haka kuma, zai iya ƙara yawan mintunan da ya buga da kuma wasannin da ya jagoranci ƙasarsa a matsayin kyaftin. A gefe guda kuma, Cristiano Ronaldo na Portugal na iya zama ɗan wasa na farko a tarihin ƙwallon ƙafa da ya buga gasar Kofin Duniya har sau shida, tare da yiwuwar zama na farko da ya zura ƙwallo a gasar har sau shida daban-daban.
Shi ma tauraron Faransa Kylian Mbappe na gab da kafa tarihi, inda zai iya zama ɗan wasa na farko da ya ci ƙwallo a wasannin ƙarshe na Kofin Duniya sau uku a jere idan ya samu nasarar yin hakan a 2026. A bangaren ƙasashe kuwa, Argentina na da damar kare kambunta kamar yadda Brazil da Italiya suka taba yi a baya, yayin da Brazil ke son ƙara yawan kofunan duniya da take da su daga biyar zuwa shida. Haka kuma Faransa na iya kaiwa wasan ƙarshe karo na uku a jere, abin da ƙalilan daga cikin ƙasashen duniya suka taba yi.
Masana harkokin ƙwallon ƙafa sun bayyana cewa gasar ta 2026 za ta kasance mafi girma a tarihin Kofin Duniya, kuma tana iya zama wata dama ta musamman ga fitattun ’yan wasa da ƙasashe su ƙara rubuta sunayensu cikin tarihin wasan. Saboda haka, duniya na sa ran ganin sabbin tarihi da manyan abubuwan tunawa yayin da gasar ke ƙaratowa.
You must be logged in to post a comment Login