Labarai
Ƙudurin samar da dokar daƙile sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a jihar Kano, ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dokokin Kano.
Ƙudurin ya kai wannan mataki ne yayin zaman majalisar na yau Talata ƙarƙashin jagorancin shugaban majalisar Alhaji Jibril Isma’il Falgore.
Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar ƙaramar hukumar Minjibur Abdulhamid Abdul ne ya gabatar da karatun dokar tare da abubuwan da ta ƙunsa.
Yayin gabatar da karatun dokar, ɗan majalisar ya ce akwai bukatar ɗaukar matakan da suka dace a jihar nan domin magance wanna matsala.
Da yake bayar da gudunmawa dangane da samar da dokar, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Takai Kwamared Musa Ali Kachako, cewa ya yi wannan ƙuduri ya zo a lokacin da ya dace la’akari da irin ƙamarin ta tu’ammali da kayan maye ya yi a Kano.
You must be logged in to post a comment Login