Labarai
Kano Line ta sha alwashin samar da sabbin tsare-tsaren Sufuri

Hukumar Sufuri ta jihar Kano watau Kano Line, ta sha alwashin samar da sabbin tsare-tsaren bunkasa harkokin Sufuri.
Shugaban hukumar Alhaji Sa’id Abdullahi Shu’aibu, ne ya bayyana hakan a ya yin bayar da horo na musamman ga sabbin ma’aikatan da hukumar ta dauka su 80, tare da basu shaidar daukar aiki ta wucin gadi, da ya gudana a ma’aikatar Sufuri da ke Goron Dutse.
A nasa jawabin Kwamishinan Ma’aikatar Sufuri Barrister Haruna Isah Dederi, ya ce ma’aikatar sa za ta yi aiki kafada da kafada da Kano Line, kana ya hori sabbin ma’aikatan da su gudanar da aikin su da Amana.
Ya yin kammala horon Alhaji Sa’id Abdullahi Shu’aibu, ya jagoranci rarraba takardar shaidar kama aikin ga dukkanin wadan da aka dauka aiki, da ya hore su su zama jakadun hukumar na gari wajen ci gaban Sufurin jihar.
You must be logged in to post a comment Login