Labarai
Majalisar dokokin Kano za ta binciki yadda kananan hukumomi ke kashe kudaden tsaro

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ba Kwamitinta mai kula da harkokin Kananan Hukumomi da Masarautu umarnin gudanar da bincike kan yadda dukkanin kananan hukumomi 44 ke kashe kudaden tsaro, kuma ta umurce su da su mika rahoton su cikin makonni biyu.
Hakan ya biyo bayan kudurin gaggawa da dan majalisa mai wakiltar Ghari da Tsanyawa, Garba Yau’u Gwarmai, ya gabatar.
Yayin gabatar da kudurin, Garba Ya’u Gwarmai, ya bayyana damuwarsa kan tabarbarewar tsaro a yankin Ƴan Kamaye da ke Karamar Hukumar Tsanyawa, inda ‘yan bindiga ake zargi suka kai hari wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama.
Dan majalisar ya ce, maharan da ake zaton sun fito daga Jihar Katsina, sun mamaye al’ummar kusan makonni 3 zuwa 4 da suka gabata, inda suka kashe sama da mutane 8, ciki har da mace mai ciki da ‘ya’yanta biyu. Ya kara da cewa an kuma kashe manoma 5 a wannan hari.
Kudurin dai, ya samu goyon bayan bulaliyar majalisar, Muddasir Ibrahim zawaciki mai wakiltar Kumbotso da har ma da sauran wasu cikin mambobin majalisar.
You must be logged in to post a comment Login