Connect with us

Labarai

Gwamnatin Kano ta ƙaddamar da sabbin ababen hawa masu amfani da CNG da gwamnatin tarayya ta samar

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ƙaddamar da sabbin motocin sufuri da gwamnatin tarayya ta samar, waɗanda suka haɗa da motocin kirar safa-safa da babura masu kafa uku da masu kafa biyu masu amfani da makamashin CNG, da kuma waɗanda ke amfani da hasken rana.

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ne ya jagoranci bikin ƙaddamar da motocin, inda ya bayyana cewa wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin jihar wajen tallafawa manufofin gwamnatin tarayya na bunƙasa amfani da makamashi mai tsafta da kuma rage dogaro da man fetur.

Gwamna Abba ya ce gwamnatin Kano ta himmatu wajen samar da ingantaccen tsarin sufuri wanda ba wai kawai zai rage wa al’umma wahalar zirga-zirga ba, har ma zai taimaka wajen rage tsadar sufuri tare da kare muhalli daga gurɓacewa.

Ya ƙara da cewa amfani da motocin CNG da na hasken rana zai taimaka wajen rage hayaƙin da ke haifar da gurɓacewar iska da kuma dumamar yanayi, lamarin da ke barazana ga lafiyar jama’a da muhalli.

A nasa jawabin, shugaban shirin CNG na ƙasa, Barista Isma’il Ahmad, ya ce shirin na daga cikin manyan tsare-tsaren gwamnatin tarayya na samar da sauki a fannin sufuri a fadin ƙasar nan.

Inda Ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na ƙoƙarin ganin an samar da hanyoyin sufuri masu sauƙi, tsafta, da kuma araha ta hanyar amfani da makamashi wanda zai rage kuɗin gudanar da sufuri idan aka kwatanta da amfani da man fetur ko dizal.

Barista Isma’il Ahmad ya ce motocin da aka ƙaddamar za su taimaka wajen rage kuɗaɗen sufuri da jama’a ke kashewa a kullum, baya ga samar da guraben ayyukan yi ga masu tuƙi, masu gyara ababen hawa da sauran masu ruwa da tsaki a harkar sufuri.
Haka kuma, ya ce shirin zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasa ta hanyar rage yawan kuɗaɗen da ake kashewa wajen shigo da man fetur da sauran makamashi daga ƙasashen waje.

Ana sa ran sabbin motocin za su fara aiki nan ba da jimawa ba domin bai wa jama’a damar more sabuwar hanyar sufuri mai araha, tsafta, da kuma kare muhalli a jihar Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!