Kiwon Lafiya
Hukumar Lura da lafiyar ababen hawa ta jihar Kano V.I.O ta ja hankalin jama’a da su ringa bin ka’idojin koyon tuki da gwamnati ta tanadar tare da samun shaidar tabbatar da iya tuki daga hukumar V.I.O kafin mutum ya fara auka kan kwalta da abin hawa.
Daraktan hukumar a nan Kano Garba Abdu Gaya ya yi jan jankalin yau jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.
Garba Abdu Gaya ya kara da cewa hukumar sa na iya kokarinta wajen tabbatar da lafiyar ababen hawa don kare aukuwar hadura.
A nasa bangaren Shugaban Kungiyar ‘yan Tifa reshen jihar Kano Mamunu Ibrahim Takai ya ce, a kokarinsu na wayar da kan ‘yan Tifa a jihar Kano kungiyarsu ta shirya wata horaswa ta musamman ga direbobin Tifa wanda hukumar V.I.O zata ringa gudanarwa don rage aukuwar haduran da masu Tifa ke haddasawa.
Hukumar ta V.I.O ta kuma yi kira ga jama’a da su rika tabbatar da ingancin ababen hawansu kafin yin amfani da su a kowacce rana, a yayin da ita kuma kungiyar ‘yan Tifa ta yi kira ‘ya’yanta da su ci gaba da baiwa hukomomi hadin kai don samun ci gabansu dama jihar Kano baki daya.